Dan Daudu anyi asara: An kama wani gardi dake yin shigar mata yana yaudarar Samari
An kama wani katoton gardi daya shahara wajen yin shigar mata domin yaudarar maza, kuma zakara na bashi sa’a yana samun nasara, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an samu tabbacin wannan matashi ya sha karban kudaden samari sanadiyyar wannan shigar a cuci maza daya keyi.
KU KARANTA: Tsofaffin ɗalibai sun karrama malamansu a garin shugaban ƙasa Buhari (Hotuna)
An ruwaito wanann matashi ya kan yaudari maza ne ta hanyar tsayawa a gefen titi, inda yake tsayar da motoci musamman motocin gayu domin a rage masa hanya, daga nan ne fa sai ya fara tattausa murya kamar macen gaske.
Daga karshe wannan matashi ya bayyana yadda yake fara samun dama akan mazan shine ta hanyar lambar wayoyinsu, daga sai ya cigaba da yaudarar wawaye daga cikin maza.
Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng