Tsofaffin ɗalibai sun karrama malamansu a garin shugaban ƙasa Buhari (Hotuna)

Tsofaffin ɗalibai sun karrama malamansu a garin shugaban ƙasa Buhari (Hotuna)

Tuna baya aka ce shine roko, inji malam Bahaushe, wannan shine kwatankwacin abin daya wakana a satin data gabata a makarantar sakandari, ta kwalejin gwamnatin tarayya dake garin Daura, jihar Katsina.

Tsofaffin daliban wannan makaranta, na shekarar 2007 ne suka shirya wata gagarumar taron sada zumunci don bikin cikar su shekaru goma cif cif da kammala wannan kwaleji, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Ba’a barin mu a baya: Gwamnonin PDP zasu kai ma Buhari ziyara a Landan

A yayin taron, kungiyar tsofaffin daliban ta karrama kafatanin ilahirin Malaman makarantar ta hanyar mika musu lambar girmamawa, sa’annan ta karrama wani malami daya tilo daya fi dadewa yana bada gudunmuwa a kwalejin.

Tsofaffin ɗalibai sun karrama malamansu a garin shugaban ƙasa Buhari (Hotuna)
Malaman da aka karrama

Bugu da kari, kafin wannan biki, kungiyar ta gabatar da taron bita ga daliban kwalejin, don fahimtar dasu muhimmancin kasancewa dalibai kuma yan kasa na gari, hakazalika tsofaffin daliban sun sake shirya wani bita ga daliban aji 3 da 6 don koyar dasu dabarun cin jarabawa, da kuma na samun gurabe a makarantun gaba da sakandari.

Wani ban sha’awa shine ba’a watse taron ba sai da tsoffin daliban suka karrama dalibai mafi hazaka a fannoni daban daban daga azuzuwa daban daban, da kuma daliban da aka yi ittifakin sun fi sauran dalibai ladabi da biyayya daga bangaren maza da mata.

Tsofaffin ɗalibai sun karrama malamansu a garin shugaban ƙasa Buhari (Hotuna)
Malaman da aka karrama

A daya hannun kuma kungiyar ta shirya wasan kwallon kafa na sada zumunta tsakaninta da kungiyar kwallon kafa ta kwalejin, inda aka tashin canjaras, ci 3 da 3, sai dai wasa ya kayatar, kuma tsofaffin daliban sun baiwa kungiyar kyautan kwallaye guda 3.

Daga karshe musulmai daga cikin tsofaffin daliban sun dauki gabarar gyara Masallacin daliban kwalejin, inda a nan take aka tattara makudan kudade da za’a kashe don gyaran da kuma siyo na’aurar kirar Sallah.

Tsofaffin ɗalibai sun karrama malamansu a garin shugaban ƙasa Buhari (Hotuna)
Shugaban kungiya, Malam Yusuf Madugu

Daga karshe shugaban kwalejin ta bakin mataimakiyarsa ya jinjina ma kokarin da tsofaffi daliban suka yi, da kuma dawainiyar da kungiyar take yi da makarantar. Suma sauran malaman makarantar na da dana yanzu sun shiwa tsofaffin daliban albarka.

Ga sauran hotunan kamar haka:

Tsofaffin ɗalibai sun karrama malamansu a garin shugaban ƙasa Buhari (Hotuna)
Mahalarta bikin tare da daliban makarantar

Tsofaffin ɗalibai sun karrama malamansu a garin shugaban ƙasa Buhari (Hotuna)
Mahalarta taron

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Satar amsar jarabawa, laifin wane ne?

Asali: Legit.ng

Online view pixel