Dubi hotunan jami'an gwamnatin jihar Kaduna a Hayin Mallam Bello
Gwamna Nasir El-Rufai ya umurci kwamishinan harkokin mata da ayyukan cigaba na jihar Kaduna Haj. Hafsat Mohammed Baba da kuma Kwamandan Operation Yaki na jihar Kaduna, Col. Yakubu Y. Soja (mai marabus) da su hallarci wani taron jin ra’ayoyin mutane domin magance matsalolin da ke adabar mutanen unguwan Hayin Mallam Bello da ke garin Kaduna.
Garin Hayin Mallam Bello dai tana tsakiyan jihar ne kuma ta bule zuwa unguwar Kabala West da Narayi.
Sarkin Hayin Mallam Bello, Alh. Kabiru Isa Gangarida ya tattaro dimbin masu ruwa da tsaki a domin su bada gudumawar su wajen shawo kan matsalolin da ke adabar unguwar.
Shugaban kwamitin ilimi na unguwar Mal. Suleiman Adamu yayi Magana akan irin hubasa da mutanen garin ke yi wajen habaka illimi da kuma irin taimakon da gwamna El-rufai yake basu ciki harda taimaka masu da fili domin ginin makaranta.
KU KARANTA KUMA: Sharhi: Shin waye zai lashe zaben 2019 tsakanin APC da PDP?
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng