Ka taba jin labarin wani Gwamna da Buhari ya daure na shekara 300
- Sabo Bakin-zuwo yayi Gwamnan Jihar Kano a shekarar 1983
- Bakin-zuwo ya buge Abubakar Rimi ya hau kujerar Gwamna
- Sai dai bai je ko ina ba Janar Buhari yayi juyin mulki a Kasar
Wanene Sabo?
Sabo Bakin-zuwo yayi Gwamnan Jihar Kano na dan lokaci a shekarar 1983 bayan ya doke abokin hamayyar sa Gwamna Abubakar Rimi bayan Rimi ya sauya sheka. Asali iyayen Sabo mutanen Kasar Neja ne su ka tare a Kano.
Tsohon Gwamnan Kano da Buhari
Kafin zama Gwamna
Kafin nan Sabo yayi Sanata a shekarar 1979 inda ya tabuka abin kirki a Majalisar. Sabo ya wakilici Kano ta tsakiya ne a lokacin daga shekarar 1979 zuwa 1983.
KU KARANTA: Manyan ayyukan da Osinbajo yayi a makon jiya
Gwamnan Jihar Kano
Sabo ya zama Gwamna a karkashin Jam'iyyar PRP bayan ya doke Abubakar Rimi. Sabo ya kawo sauye-sauye a lokacin sa daga ciki har da rusa wasu Masarautu.
Karatun Boko
An ce Sabo bai taba karatun Boko ba amma dai yace yayi karatun sa ne a gidan babban Dan siyasar nan Malam Aminu Kano. Bakin-zuwo dai yayi aikin kamfe ta kafafen rediyo.
Zuwan Janar Buhari zuwa gidan Yari
Janar Buhari ya kifar da Gwamnatin kasar a karshen shekarar ta 1983. Janar Buhari ya kama manyan 'Yan siyasar Kano da dama ciki har da Gwamna Sabo. An samu kudi kusan Dala Miliyan 10 a wannan lokaci a gidan sa. Gwannan yace dai kudin Jihar Kano ne ya adana a gidan sa. Shugaban kasar Janar Buhari ya yankewa Sabo Bakin-zuwo da wani Kwamishinan sa shekaru 300 a gidan yari.
Mun tsakuro wannan tarihi daga https://abiyamo.com
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Sanata Uba ya karbi tikitin APC
Asali: Legit.ng