To fa! Tsadar filawa na shirin sa masu sana'ar burodi shiga yajin aiki

To fa! Tsadar filawa na shirin sa masu sana'ar burodi shiga yajin aiki

Kawo yanzu dai masu sana'ar yin Burodi a arewacin Najeriya sun fara bayyana aniyar su ta shiga yajin aikin sai baba ta gani idan har farashin filawar da yayi tashin gworon zabo bai sauko ba.

Yanzu haka dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu, farashin buhun filawa ya tashi daga Naira 9000 zuwa 10000 ne ya zuwa har Naira 14,500 wanda masu gidajen biredin ke ganin yayi masu tsada.

To fa! Tsadar filawa na shirin sa masu sana'ar burodi shiga yajin aiki
To fa! Tsadar filawa na shirin sa masu sana'ar burodi shiga yajin aiki

Legit.ng dai ta samu kuma gada daya daga cikin masu saida filawar mai suna Alhaji Abubakar ya shaidawa majiyar mu cewa tashin farashin kudin motar dake yi masu dakon daga Legas zuwa arewacin Najeriya.

Ya bayyana cewa kuma a sakamakon karyewar gadar Tatabu shine dalilin karin tsadar filawar a yankin arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng