Kotu ta jefa wata matar aure gidan kaso saboda ta yi cikin shege

Kotu ta jefa wata matar aure gidan kaso saboda ta yi cikin shege

- Yadda kotu a Abuja ta jefa wata matar aure gidan kaso saboda tayi cikin shege

- Alkali ya yanke mata hukuncin daurin har na tsawon watanni biyu

A ranar juma'ar yau, wata kotu mai sunan Karmo ta jihar Abuja ta yankewa wata mata Rose James, mai shekaru 23, hukuncin dauri a gidan kaso har na tsawon watanni biyu.

Alkalin da ya yanke hukuncin wannan mata, Alhaji Abubakar Sadiq ya baiwa wannan mata zabin watanni biyu a gidan kaso ko kuma ta biya diyya ta N10 000 a maimakon zaman da za tayi a daure.

Alhaji Abubakar ya shawarci wannan mata Rose, da ta guji aikata laifuka irin wannan a gaba, don kyawawan dabi'u su ne abin koyi da wasu za su gani su yi sha'awa, amma laifuka irin wannan su na gurbata tarbiyar al'umma.

Kotu ta jefa wata matar aure gidan kaso saboda ta yi cikin shege
Kotu ta jefa wata matar aure gidan kaso saboda ta yi cikin shege

A yayin da ake gabatar da laifinta ga alkali, Rose wadda mazauniyar Karmo ce a garin Abuja, ta roki kotu da sassauci wajen hukuncin da za a yanke mata kuma tana tuhumar mijnta da jefa ta cikin aikata wannan laifi.

KU KARANTA: Yadda masana kiwon lafiya su ka fara magance cutar sikila a jikin dan Adam

Tace, mijinta ba ya kyautata mata kuma ba ya bata hakkokinta na aure da suka rataya a wuyansa, amma wanda ya yi mata wannan ciki ya dauke tamkar matarsa saboda irin dawainiya da kulawa da yake bata, kuma daman ta bayyanawa 'yan uwan mijinta tana son ya sake ta.

Jami'in dan sanda mai shigar da kara, Zannah Dalhatu, ya bayyanawa kotu cewa, a ranar 17 ga watan Yuli ne, mijin wannan mata, James Olanga ya yi karart a ofishin 'yan sanda na Karmo, inda ya bayyanawa 'yan sanda cewa matar shi tana kwanciya da wani kuma har ta samu juna biyu.

Zannah ya bayyawa koyu cewa, Rose ta amsa laifinta a yayin bincike, sai dai wannan laifi ya na da hukuncinsa a karkashin sashe na 387 na tsarin dokar kasar nan.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na facebook ko twitter a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng