Daki daki: Yadda Buhari ya fara rashin lafiyar a bana

Daki daki: Yadda Buhari ya fara rashin lafiyar a bana

A ranar 7 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi zuwa kasar Birtaniya don samun kulawa daga wata cuta dake damunsa wanda ba’a bayyana ba.

Har zuwa wannan lokaci dai ba’a ji duriyar shugaban kasar ba, face muryarsa da aka jiyo yana yi ma Musulman Najeriya barkada Sallah yayin bikin salla karama, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Ina Najeriya ta dosa? Kwanaki 75 tun bayan ficewar shugaba Buhari neman lafiya a Landan

BBC Hausa ta ruwaito jerin abubuwan da suka faru da shugaban kasa Muhammadu Buhari tun a farkon shekarar 2017, kamar haka:

Daki daki: Yadda Buhari ya fara rashin lafiyar a bana
Buhari

A ranar Alhamis 19 ga watan Janairu ne shugaba Buhari ya fara fita zuwa Landan domin jinya.

A ranar Lahadi 5 ga watan Feburairu ne shugaba Buhari ya nemi karin hutu daga majalisun dokokin kasar nan.

A ranar Juma’a 10 ga watan Maris ne shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya.

Sai dai bai samu halartan zaman majalisar zartarwa ba na ranar Laraba 26 ga watan Afrilu.

Haka zalika shugaba Buhari bai halarci sallar juma’a ta ranar 28 ga watan Afrilu ba.

Bugu da kari an sake kwatawa a ranar Laraba 3 ga watan Mayu inda nan ma ya gaza halartan zaman majalisar zartarwa.

Cikin ikon Allah sai gashi a ranar Juma’a 5 ga watan Mayu shugaba Buhari ya samu karfi, har a ya halarci sallar Juma’a.

Sai kuma ranar Lahadi 7 ga watan Mayu ya sake yin sallama da yan Najeriya, inda ya garzaya kasar Birtaniya don duba lafiyarsa a birnin Landan.

Tun wannan lokaci ba’a sake jin duriyarsa ba sai a ranar Lahadi 25 ga watan Yuni, inda ya aiko da sakon barka da Sallah ga Musulmai, sai kuma ranar Talata 11 ga watan Yuli, ranar da Osinbajo ya samu ganawa da shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Wa ya kamata yafi albashi tsakanin Malami da Likita?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng