Mahmud Abacha tare da matarsa sun samu karuwa
Allah ya albarkaci dan tsohon shugaban kasa Marigayi Sani Abacha da samun karuwa.
Mahmud Abacha wanda ya kasance da na hudu a cikin ‘ya’yan marigayi tsohon shugaban kasa Sani Abacha tare da matarsa sun haifi ya mace.
Ma’auratan wanda suka raya sunnah a shekarar 2013 sun samu karuwar ne a kasar Faransa a ranar Lahadi 16 ga watan Yuli.
KU KARANTA KUMA: Yaron da aka fara yi ma dashen hannu a duniya
Wannan kyautar da Allah ya yi masu shine na biyu domin a shekarar 2016 Allah ya basu haihuwar ‘yar su ta fari mai suna Maryam Alyaanah, wacce ta ci sunan kakarta, Hajiya Maryam Abacha.
Sai muce Allah ya raya abunda aka samu.
https://business.facebook.com/naijcomhausa/#
https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna son bamu shawara ko bamu labarai tuntube me a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng