Allah sarki: Wani Dan wasan Ajax ya gamu da cutar kwakwalwa

Allah sarki: Wani Dan wasan Ajax ya gamu da cutar kwakwalwa

- Kwakwalwar wani babban Dan wasan Ajax tayi raga-raga

- Babban Dan wasan ya samu wannan larura ne a filin wasa

- 'Yan kwallon Duniya su na ta aika sakonnin jinya ga Dan wasan

Kwanaki kun ji labarin cewa wani Dan wasan Ajax ya kife ana tsakiyar kwallo. Yanzu dai ta tabbata cewa Kwakwalwar wannan Dan wasan ta samu matsalar da ba zai warke ba.

Allah sarki: Wani Dan wasan Ajax ya gamu da cutar kwakwalwa
Wani Dan wasan Ajax Abdelhak Nouri

Kwanan nan mu ka samu labari cewa kwakwalwar Dan wasa Abdelhak Nouri na Kungiyar Ajax tayi dameji. Bisa dukkan alamu dai wannan ba karamar lalura bace wanda ba ma wasan kwallon kafar kadai za ta hana sa ba.

KU KARANTA: Abin da ya hana Adaam Zango aure

Allah sarki: Wani Dan wasan Ajax ya gamu da cutar kwakwalwa
Kwakwalwar Dan wasa ta buga ana wasa

Kungiyar sa ta Ajax da ke kasar Holand dai wannan abu bai ma ta dadi ba. Haka sauran manyan 'Yan wasan Duniya sun aika sakon addu'o'in su ta kafafen zamani irin su Tuwita ga wannan mashahurin Dan wasa da Iyalin sa.

Dan wasan tsakiyar na Ajax Abdelhak Nouri ya fadi ne bayan an kusa doka Minti 70 da take wasan da ake karawa ta Kungiyar Werder Bremen na kasar Jamus kwanaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Su wa su ka fi yaudara a gidan aure

Asali: Legit.ng

Online view pixel