So ko hauka? Tsananin soyayya ya jefa wata budurwa gidan yari, zaman wata 7 (KARANTA)

So ko hauka? Tsananin soyayya ya jefa wata budurwa gidan yari, zaman wata 7 (KARANTA)

- Budurwa ta kwashi kudin maigidanta ta kai ma saurayinta

- Alkali ya yanke mata hukuncin watanni 7 a gidan yari

Wani mutumi dan kasuwa mai suna Godwin Ola ya shigar da karar wata budurwa mai yi masa tsaron shago wajen Yansanda, inda yace ta kwashe masa cinikin shago, inda ta kashe ma saurayinta su duka.

Daily Trust ta ruwaito jami’in dansanda mai kara Mista Ashashim Helen ya garzaya da wanda ake kara tare da wanda ya shigar da kara gaban kotun Majistri dake Area 1, Karu, Abuja a ranar Talata 18 ga watan Yuli.

KU KARANTA: Dubun ɓarawon dake satar kudaden jama’an da hatsari ya rutsa dasu ta cika

Godwin ya shaida ma kotu cewar ya taba daukan wanda ake kara aiki a matsayin yar tsaron shago, inda ya umarce ta data dinga rubuta masa dukkanin cinikin da akayi a kowane rana, amma yar aikin ta ki bin umarnin ta.

So ko hauka? Tsananin soyayya ya jefa wata budurwa gidan yari, zaman wata 7 (KARANTA)
An kama ta

Ana cikin haka ne sai yar aikin ta kwashe kudi har N62,000 ta kai ma saurayinta, kamar yadda wanda ake kara ta shaida ma yansanda da kanta, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Bayan sauraron karar, sai alkali Hassan Ishaq ya yanke ma budurwar wata 7 a gidan yari, ko kuma ta biya taran N18,000, sa’annan ya umarce ta data biya maigidanta N62,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Idan gwamnati naso in zama barawo sai in zama, inji dan Najeriya Kalla:

Asali: Legit.ng

Online view pixel