HIRA TA MUSAMMAN: Zantawarmu da dattijo mai shekara 150 da haihuwa a jihar Adamawa (hotuna, bidiyo)
Arzikin da Allah ke yiwa bayinsa ya kasu iri-iri. Wadansu arzikin yaya,wasu na dukiya,wasu illimi wasu kuma yawan shekaru Allah ya azurtarsu dashi.
Wani bawan Allah mai suna Alh. Mu'azu Aliyu mai kimanin shekaru dari da hamsin da watanni goma sha daya game da cewar Malama Saudatu diyar malam Mu'azu na zaune ne anan karamar hukumar Girei dake Jihar Adamawa,arewa maso gashin Najeriya.
A hirar Legit.ng Hausa da shi Malam Mu'azu dai har a lokacin wannan rahoto na ciki hankalisa kuma yana iya gane dukkan wanda zai yaziyarce shi,Kana kuma zai yi rattala tilawar Kur’ani mai girma.
Azantawarmu da,mai anguwar kabawa, Malam Musa Wakili, wanda dan uwa ne ga malam Mu'azu ya bayyana cewa, rayuwar dan uwan nasa abun al-ajabi ne ,lura da cewa duk da yawan shekaru amma bai hanashi yin limanci a masallacin dake kofar gidansa ba kuma dama can limamin babban masallcin juma'ane dake vonokilan hayin gada.
Malam Mu'azu yakasance mai sana'ar na duke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai taras wato noma da kiwo kasancewarsa dan kabilar hausa bakabe masu asali daga jihar kebbi a arewa maso yammacin Najeriya.
KU KARANTA: Osinbajo ya isa jihar Zamfara
Malam Mu'azu Aliyu dai ya auri kimani mata guda bakwai 7 a tsawon rayuwasa kamar yadda mai dakinsa malama Lami ta shaida kadai ce ta rage cikin matansa. Allah ya kara tsawon rai ami albarka kuma yasa mu cika da kyau da Imani.
https://business.facebook.com/naijcomhausa/#
Asali: Legit.ng