Yadda na kashe mijina tare da taimakon abokina – Inji Uwargida
Wata mata, Omotayo Salawudeen ta bayyana yadda ta hada baki da wani abokinta Dolapo Oladapo suka kashe mijinta mai suna Alhaji Hakeem Salawudeen.
Legit.ng ta ruwaito yansandan jihar Osun sun samu nasarar cafke matar tare da abokin aika aikan nata, inda ta bayyana ma yan Jarida cewa a daren da zata kashe mijin nata, sai da suka yi rayuwar aure.
KU KARANTA: An miƙa koke ga jam’iyyar PDP akan lallai ta hukunta Sanata Sheriff
“Ni na gayyato Dolapo yazo ya kashe mijina, shekaru 17 muka yi dashi muna tare, kuma yayan mu 3, a gaskiya ban san abinda mijina yayi min ba, bai taba bata min rai ba, don haka nayi nadamar abin dana aikata.” Inji ta
Shima abokin matar, Oladapo, ya tabbatar ma yan jaridu cewa shi da kansa ya daba ma Alhji Hakeem wuka, bayan matar tasa ta rufe masa fuska da pillow, Oladapo ya bayyana cewa ya aikata hakan ne bayan matar tayi masa alkawarin zata bashi duk abinda ya bukata idan ya yar da bukatar ta.
Shima kwamishinan yansandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace sun fara gudanar da bincike, kuma zasu mikasu ga kotu da zarar sun kammala binciken.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Taron PDP a Abuja:
Asali: Legit.ng