Babbar magana! Yan asalin garin Abuja sun yi kazamar zanga-zanga
Wasu gungun matasa da tsaffi mata da maza da sukayi ikrarin cewa sune yan asalin garin Abuja sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a birnin tarayya na Abuja.
Yan asalin na Abuja sun yi zanga-zangar ne domin mika bukatar su ga gwamnatin tarayya wajen cewa suma suna so su rika zaben Gwaman kamar kowace jiha dake a kasar.
Legit.ng ta samu labarin cewa matasan da suka yi wannan gangamin sunyi shi ne a karkashin wata kungiyar su da suka sawa suna Inhabitants Development Association of Abuja (OIDA) a turance.
A yayin zanga zangar shugaban kungiyar Danladi Jeji yayi bayani mai tsawo inda kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta basu dama su rika zaben su don gwamanati bata tabuka masu komai.
Shugaban yayi alkawarin cigaba da fafutukar ganin an ceto yan asalin birnin ta hanyoyin da kundin tsarin mulkin kasa ya amince dasu.
Asali: Legit.ng