Wani Mutumi ya bar Matar sa mai shekara 60 a kan ta haifa masa yaro

Wani Mutumi ya bar Matar sa mai shekara 60 a kan ta haifa masa yaro

- Abin mamaki 'Yar shekara 60 a Duniya ta haihu

- Wannan mata ta dade tana neman haihuwa ba rabo

- Sai dai Mijin ta ya bar ta yace ba zai iya fama da yaro

Wata mata mai shekara 60 a Duniya ya samu haihuwa bayan ta dade tana nema amma Ubangiji bai nufa ba. Sai dai Mijin ta kuma ya tsere bayan da ya fahimci cewa ta sauka.

Wani Mutumi ya bar Matar sa mai shekara 60 a kan ta haifa masa yaro
Ikon Alah: 'Yar shekara 60 ta haihu

Mijin wannan mata Serif Nokic mai shekaru 68 a Duniya yace a wannan shekaru na sa ba zai iya famar kula da jinjiri ba don haka ne ma ya gudu ya bar Matar ta sa a lokacin da ya ji kukan wannan jariri.

KU KARANTA: Boko Haram sun sauya salon barna

Wani Mutumi ya bar Matar sa mai shekara 60 a kan ta haifa masa yaro
Hoton Serif Nokic daga Jaridar The Sun

Atifa Sheriff dai ta ji dadin samun haihuwar har ba ta damu da rashin Mijin na ta ba wanda ya bar ta zuwa Kasar Turkiyya. Wannan abu ya faru ne a Garin Novi Pazar da ke Yammacin Kasar Sabiya.

Ku na da labari cewa Sabon Shugaban kasar Afrika Emmanuel Macron ya soki mutanen Afrika musamman bakake inda yace har yanzu su na da matsala na zazzago 'ya 'ya rututu kamar yadda mu ka samu labari.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Boko Haram sun yi awon gaba da wasu mata

Asali: Legit.ng

Online view pixel