Kwalejin Jihar Gombe ta zartar da dokar "Babu Albashi ga Rashin aiki" wa lakcarori masu yajin aiki

Kwalejin Jihar Gombe ta zartar da dokar "Babu Albashi ga Rashin aiki" wa lakcarori masu yajin aiki

- Lakcarorin dai sun fara yajin aikin ne tun 11 ga watan yuli a yayinda suka nemi a biyasu basursukan kudaden su da masu fada aji na makarantar suka rike musu

- A ranar 19,ga watan afrilun shekarar 2017, ne kungiyar ta COEASU suka tunkari jami'an makarantar da bukatocin da aka kasa amsa musu

Majibinta lamarin Federal College of Education (Technical) ta jihar Gombe sun zartarda dokar rashin biyan albashin rashin aiki sakamakon yajin aiki da lakcarorin makarantar suka fara, jawaban sun bubbugo ne daga Ibrahim Shehu, Daraktan Establishment and Council Affairs na makarantar a ranar lahadi a Jihar gombe.

Lakcarorin dai sun fara yajin aikin ne tun 11 ga watan yuli a yayinda suka nemi a biyasu basursukan kudaden su da masu fada aji na makarantar suka rike musu.

Shehu ya kwatanta yajin aikin da ya jagorantu karkashin kungiyar Academic Staff Union (COEASU) reshen makarantar da cewa bai daceba.

Kwalejin Jihar Gombe ta zartar da dokar "Babu Albashi ga Rashin aiki" wa lakcarori masu yajin aiki
Babbar kofar shiga kwalejin Jihar Gombe

Ya kara da cewa masu fada ajin makarantar basu da zabin abinyi inba zartar da irin wannan hukunci da suka dauka ba don cinma tsare-tsare da ka'idojin gwamnatin tarayya baki daya, musamman lura da yanayin kunci da rashin zagayar kudi a kasa baki daya.

Shehu yace rikicin yajin aikin ya ya fara ne bada dadewa ba bayan nada sabarbin shuwagabannin kungiyar ta COEASU a watan afrilun shekarar nan

A ranar 19,ga watan afrilun shekarar 2017, ne kungiyar ta COEASU suka tunkari jami'an makarantar da bukatoci da suka kunshi neman karbar basursuka,Peculiar Academic Allowance, tareda shigar da Allowance din cikin Albashinsu na gaba, da sauransu.

KU KARANTA: Ýar kunar bakin wake ta hallaka masu bauta 10 a masallacin Maiduguri

Jami'an makarantar a lokacin tayi musu bayani gamsashe gameda yanayin karfin ita kanta makarantar da iya abubuwan da zata iya nakusa don magance koke-koken nasu da na nesa da zasuyi, harma an bada PPA and 25 per cent of the Conference Attendance Allowance (CAA) na wata daya wa ma'aikatan kuma anyi yarjejeniyar cewa a duk sanda gwamnatin tarayya ta saki kudaden promotion na 2015, za'a sallami ma'aikata bada dadewa ba.

Shehu yace dukda wannan ganawar da Jami'an makarantar sukayi da cOEASU a 20 ga watan yuni, kungiyar suyi yajin aikin jan kunne na kwanaki uku wanda ya fara daga ranar laraba 5 ga watan yuli zuwa juma'a 7 ga watan yuli, kuma daga nan suka fara yajin aikin nasu mara iyaka.

Ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

Ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel