Aure: Za a rage kudin sadaki a wani yankin Arewa

Aure: Za a rage kudin sadaki a wani yankin Arewa

- Ana shirin rage kudadden da ake biya a matsayin sadakin aure a wani yankin jihar Binuwe

- Shugaban sarakunan gargajiya a yankin Tiv ya ce tsadar aure na daga cikin abin da ke hana matasa aure

- Sarkin ya ce za su bincika dalilan da yasa kudin sadaki ke aurawa

Shugaban majalisar sarakunan gargajiya na yankin Tiv a karkashin jagorancin Tor Tiv, sarki Ochivirigh, Farfesa James Ayatse ya kafa wani kwamiti na mutane 15 don su tattauna game da yawan kudin sadakin aure da kuma tsadar bikin rasuwa a yankin Tiv da ke jihar Binuwe.

Freddie Adagbe, mai ba shugaban shawara kan kafofin watsa labari, Farfesa Ayatse ya yi wannan bayani ne a cikin wata sanarwa ga manema labarai a Makurdi fadar gwamnatin jihar a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli.

Kwamitin, wanda aka ba watanni uku domin ta gabatar da rahoto kan batun. Mai Martaba, Cif Jam Gbinde Ter Ikyor ne zai jagoranci kwamitin. Shugaban ya bukaci kwamitin da ta gudanar da bincike ta kuma gano dalilan da yasa ake samu karuwar kudin sadaki a yankin ta kuma ba da shawara kan hanyoyi da za a magance kalubalen.

Aure: Za a rage kudin sadaki a wani yankin Arewa
Tor Tiv, sarki Ochivirigh, Farfesa James Ayatse

KU KARANTA: Shekaru 10 da auren Sani Danja: Ya nuna farin cikinsa cikin wasu kyawawan hotuna

Legit.ng ta ruwaito cewa, Farfesa Ayatse ya koka cewa yawan kudin sadaki na daya daga cikin abin da ke hana matasa yin aure, sarkin ya lura da cewa a wasu lokuta wannan kalubalen na tilastawa matasan shigar neman arziki ta hanyar da bai dace ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: