Samarin Arewa sunyi wa kudu kashedi kan zaman mulki a arewa
A baya dai an sha jin wasu samari daga arewa na kokarin korar wasu kabilun kudu da ke zaune a arewa, to a yanzu kuma an jiyo su suna cewa bangaren kabilar Yarabawa lallai su mai da mayatar su domin mulki na arewa ne a wannan karon.
Kungiyar Arewa Youth Forum ta sake itar da sabuwar sanarwa, inda take kashe di ga kudancin kasar nan kan wai su maida mayatar su da tuggun su na mayar da mulki na tarayya kudancin kasar yankin kabilar Yoruba..
A cewar su, wannan karon da ma bayan 2019, duk zango ne da dole sai an baiwa arewa daama ta mulki Najeriya zango biyu, domin girmama yarjejeniya ta 'zoning' wadda jam'iyyar PDP ta kirkira
Kakakin kungiyar, Alh. Gambo Gujungu ne dai yayi wannan kira, inda yace arewar, wai ta kula da kulle kulle na kokarin amshe wa arewa mulki, domin rashin lafiyar shugaba Buhari.
DUBA WANNAN: Arewa bata isa ta hana ni magana ba, inji FFK
A irin wannan musayar kalamai tsakanin kudu da arewa dai, an sha samun takun saka da har ta kan kai ga manyan kasa sai sun tsoma baki, saboda neman hadin kan kasa.
A yanzu dai da ake fuskantar zabuka masu zuwa, hakan zai iya karuwa, musamman ganin ba lallai shugaba Buhari ya sake takara ba.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng