Dandalin Kannywood: Jarumin finafinan Hausa Sadiq Sani Sadiq ya sanya ma yarsa Asma’u (Hotuna)
- An yi bikin sunan jarumin finafinan Hausa Sadiq Sani Sadiq a ranar Asabar
- Sadiq ya sanya ma sabon yarsa Asma’u
- Ali Nuhu yana daga cikin jarumai finafinan Hausa da suka halarci zaben sunan
Fitaccen jarumin finafinan Hausa nan ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya yi bikin sunan jaririyar da Allah ya albarkace shi da ita a ranar Asabar, 15 ga watan Yuli 2017.
Sadiq Sani Sadiq da matarsa sun sanya ma jaririyar suna Asma’u. A makon da ta gabata a ranar 8 ga watan Yuli Sadiq da uwargidansa suka yi marhabi da yar.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, daga cikin fitaccen jarumai ‘yan finafinan Kannywood da suka halarci bikin sunan Asma’u sun hada da Ali Nuhu da sauran su.
KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Yadda Rahama Sadau ta fara samun ɗaukaka a harkar Fim
Allah ya raya Asma’u a kan Sunnah Anabi Muhammad (S.A.W). Amin
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng