Assha: Ta bada yaron ta an ba ta rabin buhun shinkafa da siminti

Assha: Ta bada yaron ta an ba ta rabin buhun shinkafa da siminti

- 'Yan Sanda sun yi ram da wata bayan ta kyautar da yaron ta a kan shinkafa

- Wannan Budurwa ta bada 'dan ta a madadin buhun shinkafa da siminti

- Har da wasu tebura aka hadawa wannan Budurwa mai shekara 20 a Imo

Wata Budurwa mai shekara 20 ta bada kyautar 'Dan ta inda aka ba ta rabin buhun shinkafa da kuma kudi har N200,000 da ma wasu kayan.

Assha: Ta bada yaron ta an ba ta rabin buhun shinkafa da siminti
Hoton wasu masu laifi dag Daily Post

Tuni dai 'Yan Sanda sun kama wannan Budurwa mai suna Chioma a inda abin ya faru cikin Jihar Imo. An hadawa wannan Mata har da siminti da kuma rabin dozin na kujerun zamani. Wannan mata tace shawara ce dai aka ba ta na sayar da yaron.

KU KARANTA: Shugaban NHIS ba zai bar kujerar sa ba

Chioma Fidelis tace kudin dawainiya ya gagare ta don haka kurum ta dauki shawarar saida wannan jinjiri da dama ba ta so haihuwar sa ba tun farko. ‘Yan Sanda dai tuni su kia damke wannan Mahaifiya.

Kwanaki Hukumar Kwastam da ke Legas ta bayyana cewa cikin rabin shekara ta samu sama da Naira Biliyan 130. Yanzu haka dai an dage wajen yaki da fasa kauri a Kasar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ambaliya ya tasa mutane gaba a Legas

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng