Rahama Sadau ta shirga wa BBC Hausa karya ne kan korar ta da MOPPAN ta yi – MOPPAN

Rahama Sadau ta shirga wa BBC Hausa karya ne kan korar ta da MOPPAN ta yi – MOPPAN

Fittaciyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-finai wato Kannywood, Rahama Sadau ta karyata cewar an kore ta daga kamfainin na Kannywood.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wata hira da tayi da BBC Hausa a babban birnin tarayya Abuja.

A cewar Rahama itama gani tayi kamar yadda kowa ya gani a kafafen yada labarai cewar an kore ta amma dai ita babu wanda ya aika mata rubutacciyar wasika a kan haka.

Rahma ta bayyana kamar haka: ” Ni fa babu wanda ya kore ni daga Kannywood. Har izuwa yanzu da nake Magana ba wani wanda ya aiko mani da rubutaciyyar wasika dake nuni ga sallama ta daga kamfanin.

Rahama Sadau ta shirga wa BBC Hausa karya ne kan korar ta da MOPPAN ta yi – MOPPAN
Rahama Sadau ta shirga wa BBC Hausa karya ne kan korar ta da MOPPAN ta yi – MOPPAN

“An rage gani na a shirin fina-finai ne saboda, kamar yadda na gaya maka, ina fitowa a fina-finan kudu wato Nollywood da kuma gudanar da sauran al’amura da suka danganci rayuwa ta.

KU KARANTA KUMA: Ambaliyar ruwa ya ci gidaje a Birnin Kebbi

“Amma yanzu zan koma yin fim na Hausa gadan-gadan musamman ganin irin nasarar da na samu a fim dina na Rariya. Zan ci gaba da daukar nauyin fim baya ga fitowa a ciki da zan ci gaba da yi.” Inji Rahama a hirar ta da BBC Hausa.

Sai dai kuma sakataren kungiyar dake ladabtar da ýan wasa wato MOPPAN, Salisu Mohammed ya karyata maganar Rahama. Baya ga haka ya bayyana cewa ta ce baá aika mata rubutaciyyar wasika bane kan korar tata saboda tana neman suna.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel