WAEC za ta saki sakamakon jarrabawar WASSCE a ranar Laraba
- WAEC ta ce zata saki sakamakon WASSCE na 2017 a ranar Laraba mai zuwa
- Hukumar ta bayyana cewa nan da ranar Laraba za ta saki sakamakon WASSCE na 2017
- Hukumar tace ta kirkiro 'Project 60' don inganta sashen ilimi
WAEC za ta saki sakamakon jarrabawar WASSCE na 2017 a ranar Laraba mai zuwa, 19 ga watan Yuli ko kafin ranar.
WAEC ta wallafa hakan ne a shafinta ta Facebook inda ta bayyana cewa nan da ranar Laraba za ta saki sakamakon.
Hukumar ta ce sake sakamakon jarrabawar a cikin gajerar lokacin wani bangare ne na WAEC ta sabon dabarun wanda aka sani da'Project 60'.
Hukumar tace ta kirkiro 'Project 60' don inganta sashen ilimi.
KU KARANTA: An gano wasu azuzuwan ƙasa a Zamfara inda ɗalibai ke ɗaukan darasi (HOTUNA)
Legit.ng ta ruwaito a watannin baya cewa an yi zaman jarrabawar a ranar Litinin, 27 ga watan Maris kuma ƙare a ranar 3 ga watan Mayu 2017.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng