Hausawa da Fulani sun kai karar Gwamnatin tarayya da jihar Taraba kara kotun kasa-da-kasa
- Kungiyar Fulani ta kai gwamnatin Buhari kara
- Kungiyar ta kai karar ne kotun kasa-da-kasa
- Kungiyar tace bata gamsu da yadda gwamnati ke daukar su ba
Gamayyar kungiyoyin da ke fafutukar kare hakkokin fulani da Hausawa ta maka gwamnatin tarayya da kuma jihar Taraba kotun kasa-da-kasa da zummar ganin an kwatowa yayan ta hakkokan su da aka tauye a tsaunin Mambila a kwanakin baya.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Alhaji Sale Bayere ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a garin Abuja babban birnin tarayyar ta Najeriya.
Legit.ng ta tsinkaye shi yana cewa har yanzu akwai jama'ar su da ke cikin tsaunuka da dama da ba'a kai wa wani agaji ba kuma hakan ba dai-dai bane kuma bai yi musu dadi ba.
Haka zalika ya bukaci kotun ta kasa-da-kasa da ta gaggwauta zuwa tsaunin don yin bincike kuma daga karshe ta bi masu hakkin su.
Asali: Legit.ng