Sababbin kyawawan hotunan Halima da Zahra Buhari
- Halima da Zahra Buhari sun fito cikin tsantsar kyau a wani biki da akayi kwanan nan
- Mai kwalliyar da ta tsantsara masu adon ce ta yada hotunan kyawawan matan guda biyu
- Koda dai mahaifinsu, shugaban kasar na birnin Landan inda yake jinya, sumyi kyau sannan kuma da ganinsu suna cikin farin ciki
Kyawawan hotunan ‘ya’yan shugaban kasa ya billo a yanar gizo. Dukkan sun biyun Zahra da Halima sun kasance matan aure amma wannan bai hana su caba ado da kuma hallartan taro ba.
Duk da cewar mahaifinsu a Landan inda yake jinya, hotunan Zahra da Halima ya nuna cewa tafiyar da rayuwarsu cikin inganci tare da daukar ko wace rana kan yadda ta zo. Mai kwalliya, Hermossa ta yada kyawawan hotunan ‘ya’yan shugaban kasar sannan mutane na ta magana kan kyawun su.
KU KARANTA KUMA: Ka ji kudin da kwastam ta samu cikin ‘yan watanni
Sunyi shiga iri guda sanye da dankwalin gwagwaro fari wanda ya kara fito da annurin fuskarsu.
A baya Legit.ng ta rahoto yadda kyawawan yaran suka kece raini a bikin dan Gwamna Amosun da akayi kwanan nan.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng