Real Madrid ta bada aro wani babban Dan wasan ta

Real Madrid ta bada aro wani babban Dan wasan ta

- 'Dan wasan Real Madrid James Rodriguez ya tafi Bayern Munich

- Dan wasan zai bugawa Kungiyar a aro na shekaru biyu

- Ta kai James Rodgriguez ba ya buga wasa sosai a Madrid

Fitaccen 'Dan wasan Kungiyar Real Madrid na tsakiya James Rodriguez ya tafi Kungiyar Bayern Munich inda zai bugawa Kungiyar wasa amma a aro na shekaru biyu.

Real Madrid ta bada aro wani babban Dan wasan ta
Real Madrid ta bada aro James

Babban Dan wasan na kasar Kolumbiya James Rodriguez ya bar Kulo din ne bayan ta kai ba ya buga wasanni a Madrid duk da cewa an sayo ‘Dan wasan ne da tsada daga Kungiyar Monaco ta kasar Faransa.

KU KARANTA: Ba za mu canza suna ba - Etisalat

Real Madrid ta bada aro wani babban Dan wasan ta
Madrid ta bada aron Dan wasan Rodriguez

Wani tsohon Dan wasan Kungiyar Hugo Sanchez ya dora laifi kan Dan wasan yace bai jajirce wajen nunawa Kocin Kungiyar Zinedine Zidane cewa ya dace a rika take wasa a Kulob din da shi ba.

Ai ku na da labari cewa babban Dan wasan Duniya Cristiano Ronaldo ya fasa barin Real Kungiyar Madrid da alamu dai Tauraron ya sake shawara game da zama a Kulob din bayan takaddamar da ta faru.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin ayi wa Najeriya garambawul ko a raba ta

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng