Shugaban ISIS na Iraqi da Syria Khalifa Al-Baghdadi, ya mutu
- An kashe AlBaghdadi a kasar Siriya wato Sham
- Mayakan ISIS sun tabbatar da hakan, sun kuma ce zasu fadi sunan sabon shugaba
- Kasar Rasha ce dai tace ita ta kashe shi a harin sama tun a watan Mayu
Kasar Rasha tace ta hallaka shugaban ISIL masu ta'addanci a kasashen Larai da na Turai, a wani harin jirgin sama tun a watan Mayu, sai dai hakan bai zama wani labari ba, saboda babu tabbacin ko hakan ya tabbata a kasa.
Amma a yau, kungiyar, ta tabbatar da hakan ta kafafen iyar da sakonta, inda tace lallai gaske ne shugaban nata ya riga ya mutu, kuma suna shirye shiryen sakin sunan sabon shugabansu.
Shugaba a kungiyar dai, shi ne shugaba da sauran 'yan ta'addan duniya ke wa kallo a matsayin shugaban duniya na hakika, mai amsa suna kalifa, wanda zai tabbatar musu da adalci.
KARANTA: Wanda ya karyata Linjila, yace kagaggen littafi ne
Sai dai hakan na zuwa ne a lokuta da suke kokarin kashewa da bautar da jama'a, tare da yakin sunkuru a birane a duniya.
Yanzu dai ana ganin an samo lagon kungiyar wadda take kiran kanta da daular Islama a Iraki da Sham.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng