Wani mutum yayi ma matan aure su 7 fyaɗe a Katsina bayan ya asirce su
Jami’an rundunar Yansanda jihar Katsina sun kama wani mugun mutum mai suna Sani Idris mai shekaru 40 da laifin yi ma matan aure har su bakwai fyade bayan yayi musu asiri.
A satin data gabata ne rundunar Yansanda ta gurfanar da shi gaban kotun majistri don a yanke masa hukunci, sai dai an dage sauraron karar zuwa rana 24 ga watan Yuli, inda kotu ta aika shi gidan maza, inji rahoton Daily Trust.
KU KARANTA: Ke Duniya: Matashi ya hallaka abokinsa ta hanyar farke masa ciki don ya kwashi kayan cikinsa (HOTUNA)
Yansanda sun bayyana sunayen matan auren da Idris yayi ma fyade kamar haka: Maimunatu Muntari, Hadiza Marabar Maska, Murka, Zainab Suleiman, Mana Maryam, Mariya da Hajiya Amina Dan Dutse.
Mijin Maimuna, Muntari Samaila ne ya kai karar Idris ga Yansanda akan ya kira matarsa yana fada mata cewar wai mijinta maye ne, kuma shi yana da maganin hakan.
Abinka da mace, nan fa Maimuna ta kama hanya ta tafi gidan Idris, inda ya bata wasu jiko, wanda suka yi sanadiyyar barewar juna biyun da take dauke dashi, wata 9, da ganin haka, ba tare da bata lokaci ba, Idris yayi mata fyade.
Da aka tambayi Idris game da tuhume tuhumen dake kansa, sai ya kada baki yace ‘Eh’, inda ya amsa dukkanin laifukan da ake zarginsa da su, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kalli abinda wata budurwa take yi:
Asali: Legit.ng