Minna: Akalla mutane 11 ne ambaliyar ruwa ta halaka a Nejar

Minna: Akalla mutane 11 ne ambaliyar ruwa ta halaka a Nejar

- Akalla mutane 11 suka rasa rayukansu a wata mumunar ambaliyar ruwa a jihar Neja

- Har yanzu ba a gano gawawakin mutanen da suka mutu a ambaliyar ba

- Hukumar bada agajin gaggawa ta ce ta tura jami’an ta zuwa yankin

An samu rohoton mutuwar mutane 11 a sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta barke a Suleja da kuma karamar hukumar Tafa a yankin Jihar Nejar.

Ruwan sama da aka tafka ana yi wanda ya dauki tsawon sa'o'i biyar, tsakanin ranar Asabar da kuma Lahadi ya jawo asarar gidajen mutane yayin da wasu suka ji rauni.

Daga cikin wadanda suka mutu, mutane 9 ne ambaliyar ta kashe a yankin Checheniya da ke Suleja, mutum daya kuma a yankin Kuspa na garin, yayin da wani ya mutu a Ayin-Nassarrawa a Tafa.

Minna: Akalla mutane 11 ne ambaliyar ruwa ta halaka a Nejar
Ambaliyar ruwa a jihar Nejar: Tushen hoto: vanguardngr

Gidajen da ambaliyar ta ci karfin su, sun kasance a Kaltuma da Angwan Gwari a karamar hukumar Suleja da ke jihar Neja.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar wasu daga wadanda suka rasa rayukansu sun kasance iyali daya kuma har yanzu ba a gano gawawakin su ba.

KU KARANTA: Gwamnatin jihar nan ta Arewa ta samar da tan 110,000 na takin zamani don manomanta

Babban daraktan hukumar bada agaji na gaggawa ta shiyar jihar Neja, NSEMA, Alhaji Ibrahim Inga, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a Minna, ya ce an riga an tura jami’an hukumar a yankin tare da haɗin gwiwar yan kyauyen domin aikin ceto.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel