Teku na kokarin hadiye Jihar Legas, dubi Hotunan ambaliyar ruwa
-An shafe kwana biyu ana ruwa a garin Legas wanda hankan yayi sanidiyar ambaliyar ruwa
-Ruwan ya mamaye motocin hawa, gidaje da sauran kayan masarufi
-Mutane sunyi kira da hukumar gagawa ta kawo musu taimako
Ruwan saman mai karfi dai ya fara ne tun daren jiya har safiyar yau bai tsaya ba. Wannan yasa magudanan ruwa ta tituna duk sun chika makil da ruwa. Daga bisani ruwan ya shiga gidajen mutanen unguwar.
Mutanen da abin ya shafa dai suna ta daukan hotuna suna sa wa a shafukan sada zumunta. Ga wasu daga cikin hotunan a kasa.
Allah ya kiyaye gaba. Ameen.
KU KARANTA KUMA: Ko za'a tumbuke Osinbajo?
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng