Kana abin ka Allah yayi na shi: Gowon ya bayyana yadda ya zama Shugaban kasa
– Tsohon Shugaba Yakubu Gowon ya bayyana yadda aka yi ya samu mulki
– Yakubu Gowon ya zama Shugaban kasa yana ‘dan shekaru 31
– Yanzu haka dai ‘Dan shekara 30 bai isa ya mulki kasar ba
Tun ba yau ba Gowon ya saba cewa hadari ya jawo ya karbi mulki. Tsohon Shugaban kasar ya ce shi kan sa bai shirya Shugabanci ba. Juyin mulkin da aka yi ne ya jawo ya zama Shugaban kasar nan.
Tsohon Shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya bayyana yadda ya samu mulkin kasar kamar yadda mu ka samu labari yace kurum dai tsautsayi ne ya fado kan sa. Hausawa kan ce ka na naka, Allah na na sa.
KU KARANTA: Jiya da yau Hotunan Marigayi Dan Masanin Kano
Yakubu Gowon yace juyin mulkin da aka yi a tsakiyar shekarar 1966 da ya hambarar da Gwamnatin Sojin Janar Aguiyi-Ironsi ya ba sa damar zama Shugaban kasar. Gowon ya hau mulki ne yana shekaru kusan 30.
Janar Yakubu Gowon yayi dogon mulki har bayan Yakin basasa yana matashi ko da dai yace bai shiryawa mulkin ba. Yanzu haka dai ‘Dan shekara 30 bai isa ya zama Shugaban kasar Najeriya ba.
Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Shiru har yau: 'Yan Najeriya sun fara neman Shugaban kasar su
Asali: Legit.ng