Kasashe 10 da suka fi hadari a Duniya, Najeriya ta nawa tazo?

Kasashe 10 da suka fi hadari a Duniya, Najeriya ta nawa tazo?

- Kasashen da suka fi hadari a Duniya

- Najeriya ta zo lamba 5 a Jerin Kasashen da suka fi hadari a Duniya

- Najeriya na fuskantar matsaloli na tsaro

Wadanne Kasashe ne suka fi hadari a Duniya? Duk shekara US State department ana tantance Kasashen da suka fi zaman lafiya a Duniya. Suna bincike akan Kasashen da suka fi hadari don ‘yan Amurka masu tafiye-tafiye, da yawon bude ido.

Najeriya ta zo ta lamba 5 a cikin jerin lambobin kasashen da suka fi hadari a duniya. Ta samu gargadi 23 na ziyara saboda rashin kwanciyar hankali a Kasar daga US state department.

Kasashe 10 da suka fi hadari a Duniya, Najeriya ta nawa tazo?
Kasashe 10 da suka fi hadari a Duniya, Najeriya ta nawa tazo?

Najeriya, Mali da Syria suna cikin jerin Kasashe masu hadari saboda ta’addanci da ke afkuwa a Kasashen. Amma mutanen Amurka sun fi fuskantar barazanar rai a Kasahen Thailand, Honduras da Pakistan.

KU KARANTA KUMA: Dangote ya musa batun rashawar miliyan 100

Ofishin jakadancin Najeriya na Washington, Mr. Hakeem Balogun ya bayyana dalilai daban daban da ‘yan Najeriya suke fuskanta wajen shiga Amurka.

Shugaba Donald Trump ya hana wasu Kasashe shiga Kasar Amurka. A wata tattaunawa da aka yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya dake Washington, ya bayyana hanin bai shafi ‘yan Najeriya ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel