Noma tushen arziƙi: An samu wasu dankalin turawa masu girman Doya a Kaduna (HOTUNA)
- Noman dankalin turawa ya samu habbaka a jihar Kaduna
- An girbi dankalin da girmansa ya kai girman doya
Manoman jihar Kaduna sun fara murmusawa yayin da aka fara girbe dankalin turawan da aka shuka a kudancin jihar, kamar yadda wani ma’abocin facebook Injina Funam Kato ya bayyana.
Kamfanin sarrafa dankalin turawa mai suna Vicampro ne suka noma wannan makeken dankali a ranar Laraba 5 ga watan Yuli, inda shima kwamishinan harkokin noman jihar ya samu halartar girbin.
KU KARANTA: An yi bikin buɗe sabon ofishin hukumar EFCC na jihar Kaduna (HOTUNA)
An saba ganin dankalin turawa dan karami ne, amma sai gashi a wannan karo Vicampro ta girbe wasu irin dankali masu girman gaske, inda wasunsu sun kai girman doya.
Majiyar Legit.ng ya bayyana farin cikin al’ummar kudancin Kaduna musamman ta yadda gwamnan jihar ya baiwa kamfanin Vicampro daman yin noma a yankin, wanda yace hakan ya taimaka ma manoman yankin sosai.
Ga sauran hotunan nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wani hukunci ya dace da barayin gwamnati?
Asali: Legit.ng