Mahaukaciya da ta haihu ta samu tallafi daga gwamnati (hotuna)
- Wata mahaukaciya da ta haifi ‘ya mace ta samu tallafi daga karamar hukumar
- An dauki ‘yar da matar ta haifa zuwa gidan marayu
- An mayar da matar asibitin kwakwalwa
Wata karamar hukuma a jihar Ondo ta bayar da tallafi ga wata mahaukaciya da ta haihu a yankin Yaba dake jihar.
Legit.ng ta tattaro cewa hukumomin karamar hukumar Idanre sun kai doki ga wata mata bayan ta haifi ‘ya mace.
A cewar wani mai amfani da shafin Facebook, Jimoh Ibrahim, karkashin shugabancin mai girma Adebiyi Ayannuola, an dauki jaririyar zuwa gidan marayu.
KU KARANTA KUMA: Ina da wani buri! Kalli bidiyon Maitama Sule yana magana kafin mutuwar shi
Ibrahim ya kara da cewa an kuma dauki mahaifiyar yarinyar zuwa asibitin kwakwalwa don bata kulawa na mussaman.
Matar shugaban karamar hukumar Idanre, Doyin Ayannuola da mai kula da sashin lafiya, Aderonke Akindolire, ne suka jagoranci kula da mayar da jaririyar da uwarta inda ya kamata.
Kalli rubutun a kasa:
Abu ya yi kyau!
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng