HOTUNAN yayinda gawar Danmasanin Kano ta isa jihar Kano
- Gawar Danmasanin Kano, Alhaji Yusuf Maitama Sule ya isa jihar Kano
- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje tare da sauran manyan gwamnati ne suka tarbi gawar
- An karbi gawar Marigayin a sansanin jiragen sojojin sama dake Kano
Rahotanni sun kawo cewa gawar Danmasaini Kano kuma tsohon ministan Najeriya, Alhaji Yusuf Maitama Sule ya isa jihar Kano.
A dazu ne Legit.ng ta samu labarin isar gawar Danmasanin Kano da ya rasu a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli a kasar Masar babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban ma’aikata na tarayya, Abba Kyari, ne ya karbi gawar a ranar Talata, 4 ga watan Yuli tare da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana’izar Danmasanin Kano.
KU KARANTA KUMA: Za’ayi jana’izar Danmasanin Kano a yau Talata da Misalin Karfe hudu
Jirgin dake dauke da gawar ya iso da misalin karfe 1:54 na rana.
A yanzu dai gwamnan jihar Kano, Alhaji Umar Ganduje, tare da manyan jami'an gwamnatin tarayya da kuma na jiha suka karbi gawar Marigayin a sansanin jiragen sojojin sama dake Kano.
Ga hotunan a kasa:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng