Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta caccaki mata masu bilicin

Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta caccaki mata masu bilicin

- Jaruma Nafisa Abdullahi ta dira a kan mata masu bilicin

- Nafisa Abdullahi tace yin hakan bai dace ba

- Binciken kimiyya ma ya gano cewa man bilicin din yana haddasa cutar kansa

Shahararriyar jarumar wasan Hausa din nan watau Nafisa Abdullahi ta fito fili ta yi kasa-kasa da matan da ke anfanin da man nan mai kara fari na shafawa wato bilicin.

Jarumar ta yi wannan kakkausar suka ce a shafin ta na sada zumunta na Instagram inda tace hakan bai kamaci yar musulmai ba don kawai ta burge maza.

Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta caccaki mata masu bilicin
Dandalin Kannywood: Jaruma Nafisa Abdullahi ta caccaki mata masu bilicin

Legit.ng ta samu labarin cewa Nafisa Abdullahi tace: “Na ki yin amfani da man da ke sa fata ta yi haske ne saboda na gamsu da yadda Allah ya halicce ni. Ina murna kan hakan. Allah ya san dalilin da ya yi ni haka, don haka ba zan sauya launin fatata ba”.

Binciken masana dai ya nuna yawan masu yin Bilicin din a Afrika na dada karuwa sannan kuma yin anfani da man yana haddasa cutar kansa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel