Dubi dan-dakon da ya makale a tayar jirgi ya isa birnin Landan

Dubi dan-dakon da ya makale a tayar jirgi ya isa birnin Landan

- Ba karamin hadari bane makale wa jirgi a bi shi zuwa wta nahiya, saboda sanyin sararin samaniya na iya daskarar da mutum a cikin jirgi.

- Wani bawan Allah mai suna Emmanuel hakan yayi yaje ya makale jirgi ya rayu har zuwa birnin landan.

Ba karamin hadari bane makale wa jirgi a bi shi zuwa wta nahiya, saboda sanyin sararin samaniya na iya daskarar da mutum a cikin jirgi. Wani bawan Allah mai suna Emmanuel hakan yayi yaje ya makale jirgi ya rayu har zuwa birnin landan.

A jirgin Medview dai aka ga wannan tahaliki mai fatan tsere wa daga kasarsa Najeriya domin ya je garin turawa, domin sake sabuwar rayuwa.

Dubi dan-dakon da ya makale a tayar jirgi ya isa birnin Landan
Dubi dan-dakon da ya makale a tayar jirgi ya isa birnin Landan

KU KARANTA: Yakubu Gowon Yace a bi hanyar lumana kan batun ballewar Najeriya

Mista Debola Akingbade ne dai ya yada wannan hoto a shafinsa na dandalin facebook, inda yace, 'wannan yaro kamar maye, Emmanuel Ugochukwu, wanda daga kai kaya jirgin Medview a Lagos, kawai sai ya makale a tayar gaba har birnin Landan, duk don neman zuwa turai.

Sa'rsa dai itace gaban jirgin bayyi sanyin da zai daskaras da jininsa ba, ba don haka ba, da tuni ya zama kankara.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa

Twitter: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel