Abin da ya sa ba za a taba mantawa da Dan Masanin Kano ba
– Rasuwar Dan Masanin Kano ya bar gibi a kaf Najeriya
– Gwamnatin Kano ta bada hutu domin makokin Marigayin
– Maitama Sule yana cikin Ministocin farko a Najeriya
A kan ce da zarar an yi rasuwa to an rasa mutum, amma idan tsoho ya rasu to tarihin kasa ya fadi. Dan Masanin Kano Ambasada Yusuf Maitama yana cikin wadanda ke rike da tarihi da sirrin Najeriya.
Dan Masanin Kano ya rike mukamai da dama wanda har ya taba zama Minista yana kasa da shekaru 30. Dan Masani mutum ne da ya iya magana kwarai da gaske. Maitama ya taba zama Ambasadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.
KU KARANTA: Allah yayi wa Dan Masanin Kani rasuwa
Maitama Sule ya taba takarar Shugaban kasa a shekarar 1979 sai dai bai samu ko nasarar lashe zaben fitar da gwani ba wanda Shehu Shagari yayi nasara. Daga baya dai ya zama Ministan Shagari na dan lokaci.
Dan Masani ya taba cewa: Idan har sanin Shugabanci ne da iya jagoranci sai Bahaushe. Sanin kasuwanci kuma sai Inyamuri. Shi kuwa Bayarabe mutum ne da ke gudun tashin hankali a rayuwar sa. Ka ji Maza! Allah ya jikan sa!
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Gobara ya kama wani goda saman dutse
Asali: Legit.ng