Abubuwan tarihi 11 dangane da marigayi Dan Masanin Kano-KARANTA
- Shahararren dattijon yankin Arewa, Maitama Sule ya rasu a kasar Masar
- Kafin rasuwarsa, Maitama Sule na daya daga cikin yan Arewa masu mutunci a idon Jama’a
A yau Litinin 3 ga watan Yuli ne Allah yayi ma Dan Masanin Kano, Alhaji Maitama Sule rasuwa a kasar Masar inda ya kwashe lokaci yana jinya.
Legit.ng ta kawo muku wasu daga cikin muhimman abubuwan tarihi dangane da marigayi Maitama Sule:
KU KARANTA: Abin da ya sa ba za a taba mantawa da Dan Masanin Kano ba
1- A birnin Kano aka haife Maitama Sule, kuma yana da marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya nada shi sarautar Dan Masanin Kano.
2- An haifi Maitama Sule a shekarar 1929, kuma ya rasu yana da shekaru 87.
3- Yana da shekaru 24 ne ya zama dan majalisar wakilai, sa’annan yana dan shekaru 29 ya zama minista.
4- Shakikan aminansa sune marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, marigayi galadiman Kano, Tijjani Hashim da kuma Alhaji Aminu Dantata.
5- Shine mutumin da yafi dadewa a matsayin ministan mai ba tare da mallakar rijiyan mai ko daya ba.
6- Maitama yak ware a yarukan Hausa, Ingilishi, Larabci da Fillanci
7- Mutanen dayake koyi dasu sun hada da Tafawa Balewa, Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikwe da kuma Malam Aminu Kano.
8- Ya zama kwamishinan karban koke-koke da korafi na gwmanantin tarayya a shekarar 1976, zamanin mulkin Obasanjo na farko.
9- A shekarar 1979 yayi takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar NPN, amma ya sha kashi a zaben cikin gida a hannun Alhaji Shehu Sahagari.
10- A wannan shekarar ne aka nada shi mukamin wakilin Najeriya na dindindin a majalisar dinkin Duniya.
11- A shekarar 1983 ne ya dawo gida Najeriya, inda aka nada shi mukamin ministan daidaita sahun yan Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Shin zaka iaya agaza ma Buhari ya samu lafiya?
Asali: Legit.ng