Sojojin Najeriya sunyi sallah a filin daga (hotuna)
- Hotuna na wasu sojin Najeriya da sukayi sallar idi a filin daga ya shahara a yanar gizo
- Jajircewan sojojin ya taba zuciyar mutane da dama
An gano wasu sojin Najeriya na sallar idi a filin daga. Jajircewar jami’an kan addininsu da kuma imaninsu ya taba zukatan mutane da dama har suka yi masu fatan alkhairi da kuma addu’an Allah ya kare su.
Abu ne mai matukar kayatarwa sanin cewa wadannan mutane basu manta da Allah ba duk da kalubalan da suke fuskanta a kullun. Mun samu hotunan jaruman a yayinda suke sallah ne daga shafin Rariya.
KU KARANTA KUMA: Likitocin Buhari sun ce ba zai iya tabuka wani abu ba – Fani Kayode ya yi ikirari
Kwanaki Legit.ng ta yada hoton wani soja yana addu’a kuma hoton ya kayatar da mutane da dama. Sanin cewa wadannan mutane na sadaukar da rayukansu a kullun don kare sauran mutane.


Kalli wasu sharhi kan hoton wani sojan dake sallah a kasa:
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Kalli wannan bidiyo na Legit.ng a kasa:
Asali: Legit.ng