Labaran Kannywood: Ali Nuhu ya fitar da ƙayataccen Fim ɗinnan, Mansoor

Labaran Kannywood: Ali Nuhu ya fitar da ƙayataccen Fim ɗinnan, Mansoor

- Sarkin Kannywood ya fitar da sabon fim din kamfaninsa

- Fim din mai suna Mansoor ya fito ne a ranar Alhamis

A ranar Alhamis 29 ga watan Yuni ne Ali Nuhu, wanda aka fi sani da Sarkin Kannywood ya sake baje kolin da gwanintarsa da hazakarsa, inda ya fitar da sabon Fim, Mansoor.

A cewar Ali Nuhu ya kwashe sama da shekaru goma yana tunanin akan fim din Mansoor, sa’annan an kwashe kimanin shekaru biyu ana shirya shi da tsara shi, kuma Mansoor ya lashe kimanin naira miliyan 8 a jimlace.

KU KARANTA: Miji da mata sun taka sawun ɓarawo: An kama su da wayar wata mata da aka yi garkuwa da ita, kuma aka kashe ta

BBC Hausa ta ruwaito an kaddamar da wannan Fim ne a katafaren gidan Sinima dake jihar Kano, sa’annan daga bisani ne za’a fara sayar da fayayansa na bidiyo.

Labaran Kannywood: Ali Nuhu ya fitar da ƙayataccen Fim ɗinnan, Mansoor
Mansoor

Ali Nuhu ya shaida ma majiyar Legit.ng cewa jigon labarin Mansoor wani matashi ne da aka same shi ta cikin shege, kuma mahaifiyarsa ta ki yarda ta bayyana masa hakan, har sai da soyayya ta debe shi, inda iyayen budurwarsa suka yi masa gorin Uba.

Labaran Kannywood: Ali Nuhu ya fitar da ƙayataccen Fim ɗinnan, Mansoor
Mansoor

Daga nan ne fa ya shiga duniya neman mahaifinsa. Ali Nuhu yace muhimmin darasin cikin fim din Mansoor shine kada ka yi ma mutum gori a duk halin da ka tsince shi, sa’annan kada ka tsangwame shi.

Wasu daga cikin jaruman Fim din sun hada da Maryam Yahaya, Umar M Sharif, Baballe Hayatu, Abba El-Mustapha da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sabbin Sojojin Najeriya:

Asali: Legit.ng

Online view pixel