Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa na rage fitowa finafinan Hausa - Sani Danja

Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa na rage fitowa finafinan Hausa - Sani Danja

- Miliyoyin magoya bayan sani danja sun dau lokaci mai tsawo basuga jarumin a cikin fina finai masu fitowa ba kamar yadda sauran jarumai suke fitowa.

- Hakan yasa wakilinmu na jihar nasarawa yayi tattaki zuwa birnin lafia fadar gwamnatin jihar nasarawa inda sani danja yakai ziyarar bikin sallah.

Legit.ng ta samu labarin cewa jarumin wadda yake kewaye da jami'an tsaro yayiwa jaridar dimokuradiyya bayani dangane da rashin fitowarsa a fina finan baya bayannan kamar haka.

Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa na rage fitowa finafinan Hausa - Sani Danja
Dandalin Kannywood: Dalilin da ya sa na rage fitowa finafinan Hausa - Sani Danja

Ni mutum ne mai harkoki daban daban bawai harkar film kawai nakeyi ba, sa'amnan kuma ina wakar turanci tare da fitowa a fina finan turanci kaga ko dole fina finaina na hausa su ja baya.

Amma yazama dole a gareni da nasamu lokaci domin cigaba da fitowa a fina finanmu na hausa saboda na sharewa magoya bayana hawayensu.

Daga karshe jarumin yayiwa masoyansa na duniya fatar alkhairi tare da yi musu barka da sallah.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel