Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)

Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)

Legit.ng ta yi karo da wani labari mai karya zuciya na wani karamin yaro da malamin sa ke azabatar da shi.

A cewar wani mai amfani da shafin Facebook, yaron mai suna Hassan ya ce mahaifinsa wanda a yanzu ya rasu shine ya tura sa karatu gurin mutumin.

A yanzu jami’an yan sandan jihar Gombe sun kama malamin dake koyar da karamin yaron.

KU KARANTA KUMA: 'Yan matan Chibok 2 da suka tsere sun gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump da 'yar sa a White House

Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)
Hassan mai shekaru 6 da malamin sa ya daure shi

Wani Sheriff Almuhajir ne ya buga labarina shafin san a Facebook kamar haka:

“Daga garin Gombe, jiya wani aboki na kuma jam'in tsaro Ya kirawo ni a waya cikin bacin rai yana nuna mun halin da wani yaro Ya shiga da sunan Karatun Qurani.

Yaron sunan shi Hassan da bai wuce shekaru 6 ba, ya bayyana ma su cewa mahaifin shi ne ya kawo shi wannan gari domin Almajiranci, daga bisa ni baban ya rasu kuma bai san ina uwar shi ta yi aure ba. Ya kasance karkashin kulawar wannan Malami da ya ke azzaba shi kamar yadda kuke gani a cikin hoto.

A Yanzu dai malamin na hanun jamiah tsaro, ko da ya ke yace shi ma ajiyar yaron aka ba shi ba shine ainahin Malamin shi da ya sa a daure shi ba.

Al-ummar Arewa kenan; ana Jan hankalin su akan irin wannan zalumci da sunan Islama suna gardama, sai yaronnan ya shiga bh ya dauki bindiga yana karkashe su, sai su komo suna cewa Jonathan ne.

Allah Ya kyauta.”

Kalli karin hotunan a kasa:

Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)
Yan sandan jihar Gombe sun kama malamin nasa

Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)
Bautar da ‘ya’yan mutane da sunan karatun Al-Qur’ani (hotuna)

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na Legit.ng inda sunan Allah ya fito a jikin bishiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel