Dandalin Kannywood: Safiya Musa tayi wa sauran matan fim wa'azi

Dandalin Kannywood: Safiya Musa tayi wa sauran matan fim wa'azi

- Tun farkon fara fim din Safiya Musa ba ta shiga fim dan neman kudi ba.

- Ta shiga fim ne sabida wulakancin da wata yar fim tayi mata a Kaduna.

Tun daga wannan lokacin tayi alwashin shiga sana'ar fim. Kuma Allah taimake ta shiga sana'ar fim da kafar dama. Domin sai da ta dusashe tauraruwar jarumar da ta wulakanta ta.

Legit.ng ta samu labarin cewa karshen daina fim din Safiya Musa, ba'a son ra'ayinta ta daina fitowa a fim ba domin tauraruwarta naganiyar haskawa akayi masu korar kare su goma, ciki harda Maryam Hiya da Kubura Dako.

Bayan an kore ta ne, ta sami miji tayi aure wanda har yanzu tana gidan mijinta tareda kyawawan 'yayansu.

Dandalin Kannywood: Safiya Musa tayi wa sauran matan fim wa'azi
Dandalin Kannywood: Safiya Musa tayi wa sauran matan fim wa'azi

Ganin yanda rayuwa ta canja matane yasa tace: "Duk jarumar da ta sami miji tayi aure, idan ba haka ba akwai lokacin da zai zo ba fim din ba auren."

"Tabbas, aure lokaci amma lokacin tare suke tafiya da niya. akwai mata na kannywood wanda basu da niyar aure, amma sai suce lokacine baiyi ba" inji Safiya Musa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel