Jami’ar tarayya da ke Sokoto ta kori Malami bisa zargin musanyar sakamakon jarabawa

Jami’ar tarayya da ke Sokoto ta kori Malami bisa zargin musanyar sakamakon jarabawa

- Jami’ar Usman Danfodio Sokoto (UDUS) ta bayyana cewa ta kori wani malami a bisa zargin yin musanyan sakamakon jarabawan dalibai.

- Mataimakin shugaban makarantar watom V.C Farfesa Abdullahi Zuru, ya bayyana haka ne ga manema labarai a Sokoto a yau 24 ga watan Yuni 2017 amma ya ki ya bayyana sunan malamin.

Legit.ng ta samu labarin cewa Farfesa Zuru ya ce: “Hukumar jami’ar ta yanke wannan hukunci ne don ya zama kaman gargadi ga sauran malamai.

"An dauki wannan matakin ne domin a tunatar da malaman ilimi da kuma ma'aikatan makarantar a aka abin da zai faru idan aka kama wani daga cikin su ya aikata irin wannan laifin.

“Ba za mu bata lokaci ba wajen hukunta duk wani ma’aikaci da aka kama shi da aikata irin wannan laifin.

Jami’ar tarayya da ke Sokoto ta kori Malami bisa zargin musanyar sakamakon jarabawa
Jami’ar tarayya da ke Sokoto ta kori Malami bisa zargin musanyar sakamakon jarabawa

“Jami’ar tana da sama da dalibai 30,000 sannan akwai jagororin da aka tsara da kowa ya kamata ya bi. Ba za mu yadda a kauce ma wannan tsarin ba.

Zuru ya kuma ja hankalin daliban jamai’ar game da harkan magudi a jarabawa ba, inda ya kara da cewa jami’ar ba za a yadda a karya ita wannan doka ba.

Ya ce dole dalibai su bi su dokokin jami’ar kamar yadda aka tsara ko kuma su gamu da hukumar jami’ar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: