Dandalin Kannywood: Adam A Zango yayi sabon fim din da ba'a taba irin sa ba
Jarumi Adam A Zango ya jima yana yo fina finai wanda suka saba zuwa da sabon salo a kannywood. A bana a kuma yo wani fim wanda yasha ban bam da sauran fina finan hausa na kannywood.
Fim ne wanda ya janyo cece-kuce ga sauran daraktoci akan irin salon da fim din yazo da shi. Wasu mutanen cewa su kayi, Adam A Zango ya yi amfani da tsafi acikin fim din, amma maganar gaskiya ba wani tsafi siddabaru ne kawai na na'ura mai kwakwalwa (cumputer).
Legit.ng ta samu labarin cewa Adam A Zango ya kashe naira milliyan goma sabida fim din, domin har kasar Cameroon yaje sabida daukar fim din. Sunan fim din MADUGU wanda yasha bamban da sauran fina finan kannywood.
Tun kafuwar kannywood kawo yanzu ba'a taba yin fim mai abin al'ajabi ba kamar fim din MADUGU. Inji fasihi wanda akeyiwa lakabi da Horon Darakta Hafizu Bello.
Wannan Fim MADUGU yana da jerin fina finai takwas da Adam A Zango yace zai bada umarni a bana 2017.
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng