Hoton Atiku Abubakar a gona ya jawo abin magana a Najeriya
– Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku ya leka gona
– Atiku Abubakar dai babban manomi ne a Najeriya
– Wasu sun dura kan tsohon mataiamakin shugaban kasar
Jama’a ba su yi da sauki ba yayin da hoton Atiku a gona ya bayyana. Wasu dai sun ce yayi ne kurum don mutane su gani su kuma shaida. Jama’a a kafafen sadarwa na zamani dai sun tofa albarkacin bakin su.
KU KARANTA: An kashe Fulani da dama a Taraba
Kwanan nan mu ka samu wani hoton Tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar inda ya leka gona cikin wannan damina domin aikin noma. Mutane da ke kafafin sadarwa dai sun yi ca a kan Dan siyasar.
Wani Bawan Allah a shafin Tuwita mai suna @Jag_bros cewa yayi lallai wannan aikin gona na manya ne don kuwa ga hular sa nan a mike cikin kari ga kuma takalmin sa kal da kayan sa fyas-fyas yayin da agogon sa mai tsada yake kyalli.
KU KARANTA: Kwankwaso ya ba Shugabannu shawara
Wani kuwa cewa yayi ba mamaki irin rashin gaskiya da ha’inci Atiku Abubakar din ya ke shukawa. Wani kuma mai suna @Lemeveteran a shafin na Tuwita ya tuna masa ne cewa fa kwanan Fulani su ka kai hari a wani kauyen Yankin amma yayi tsit ko oho.
Jiya kun ji Tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Kwankwaso yace Allah ne zai yi zabi a zabe mai zuwa na 2019. Kwankwaso yace kasancewar Shugaba Buhari na asibiti ba ya nufin sauran ‘Yan siyasar sun fi lafiya.
Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Garin Nnmadi Kanu ya zama Madina
Asali: Legit.ng