Ka ji abin da zai faru da Najeriya a shekarar 2050

Ka ji abin da zai faru da Najeriya a shekarar 2050

– Harsashe ya nuna cewa yawan mutanen Najeriya zai lula

– A haka ma dai Najeriya ce ta 7 wajen yawa a Duniya

– Zuwa shekarar 2050 kasar za ta kere Amurka

Yawan mutanen Kasar Najeriya kara karuwa kurum yake yi. Nan da wani lokaci Najeriya za ta zama ta uku wajen adadin Jama’a. Kasar China da kuma India ne sahun gaba wajen yawan al’umma.

Ka ji abin da zai faru da Najeriya a shekarar 2050
Yawan mutanen Najeriya na kara karuwa

KU KARANTA: Kalmomin Hausa da aka aro daga wasu yare

Wani harsashe da wata Hukuma da ke kula da yawan Jama’a na Duniya tayi ya nuna cewa Najeriya za ta kerewa Kasar Amurka wajen yawan mutane nan da shekarar 2050. Hakan na nufin Najeriya za ta zama ta uku wajen yawan Jama’a a kaf Duniya.

Zuwa wannan lokaci dai yawan haihuwar da ake samu a Nahiyar Afrika zai ribanya wanda ake samu a halin yanzu. Zuwa shekarar 2020 adadin Jama’an Duniya dai zai kusa Biliyan 10. Yanzu dai adadin mutanen Duniyar yak era mutum Biliyan 7.6.

Kasashe irin su Najeriya da China watau Sin, Indiya, Indonesiya, Fakistan da Amurka su na cikin wadanda su ka fi yawan al’umma a Duniya.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Nnmadi Kanu da mutanen Kasar Abiya

Asali: Legit.ng

Online view pixel