Garabasa: Sunnah 10 na Manzon Allah SAW a Ranar Idi
– Musulmai na shirin murnar karamar Sallah a Duniya
– Da zarar Azumi ya kare za ayi biki a Duniyar Musulmai
– Akwai sunnoni da dama a wannan rana da ya kamata a kiyaye
Legit.ng ta kawo maku wasu sunnonin Manzon Allah a matsayin garabasar wannan shekara.
1. Wankan tsarki
Ana bukatar wankan gusul kafin a je Masallacin Idi
2. Karin safe
Yana cikin sunnah a samu wani abinci a tauna kafin a tafi Masallacin Idi a lokacin karamar Sallah.
3. Sababbin kaya
Daga cikin Sunnah ana so a sanya sababbin kaya a Ranar Sallah ko kuma mafi kyau akalla
4. Sallar Nafila
Bai halatta ayi Sallar Nafila a filin Idi ba yayin da ake jirar Liman.
KU KARANTA: Ashe Darika da Shi'a duk daya ne- Inji Babban Shehi
5. Nafila a gida
Ana kuma so ayi nafila raka’a 2 rak yayin da aka dawo daga Masallacin Idi watau a gida.
6. Sauya hanya
Yana daga cikin Sunnah a canza hanyar da aka bi wajen zuwa yayin da ake dawowa gida
7. Takawa a kafa
An so a je Masallaci a kafa ba bisa wani abin hawa ba domin zuwa Sallar Idi.
8. Gaisuwa
Sahabbai kan gaida ‘Yan uwan su yayin da su ka hadu domin murna a wannan rana.
9. Ziyara
Ziyarar ‘Yan uwa da abokan arziki na cikin Sunnah a wannan lokaci na farin ciki.
10. Kabarbari
Ana fadan Allahu Akbar, Allahu Akbar, La ilaha illalLah, Allahu Akbar, Wa lilLahil hamd.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Jama'a na fadin albarkacin bakin su game da Evans
Asali: Legit.ng