'Buhari ya gaza, ya fadi' inji Umar Ardo, hadimin Atiku

'Buhari ya gaza, ya fadi' inji Umar Ardo, hadimin Atiku

- Umar Ardo tsohon dan PDP ne, kuma na hannun daman Atiku

- Yace ba'a ma ga Buhari ba balle ace zayyi takara a 2019

- Yace bada a harkar tsaro babu wani karin katabus da Buhari yayi

A cece-kuce da 'yan siyasa kanyi a irin wannan lokaci, na shirin shiga zabuka ko takarar na-gani-ina so, an jiyo wani tsohon dan PDP kuma mai neman gwamna a jam'iyyar PDP daga jihar Yola yana bayanin irin gazawar da wai shugaba Buhari yayi a shekaru biyu da suka wuce.

A cewar umar Ardo dai, shekaru biyun nan babu wani aikin kuzo ku gani da shugaba Buhari yayi, sai ma dai bata wa jama'a lokaci da wai yayi bayan daukar alkawurra, da ya kasa cikawa.

'Buhari ya gaza' inji Ardo
'Buhari ya gaza' inji Ardo

Umar Ardo, wanda a shekarun 1999-2003 ya yi wa tsohon mataimakin shugaba Obasanjo, wato Atiku Abubakar aiki, ya taba neman takara ta gwamna a jiharsa ta Adamawa, kuma guguwar Buhari ta kada shi.

A yanzu dai yace banda harkar tsaro babu wani abu da jam'iyyar APC ke iya tutiya da shi. A kuma wata makalar, an tambaye shi ko Buhari zai yi hobbasa in ya sake neman takara, sai ya kada baki yace; "Yo wanda ba'a ma ganshi ba wata da watanni ai ba'a masa lissafin takarfa, ya ma fito jama'a su saka shi a ido mana tukun, kafin a fara wata maganar zabe."

Shugaba Buhari dai na can yana jinya a Ingila kuma ana saka rai zai iya shigar bazata zuwa gida Najeriya domin bukukuwan sallah karama.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
APC