Bayan shekaru kusan 20: Al-Mustapha ya bayyana abin da ya kashe Abacha

Bayan shekaru kusan 20: Al-Mustapha ya bayyana abin da ya kashe Abacha

– Dogarin tsohon Shugaban kasa Abacha ya bayyana abin da ya kashe sa

– Al-Mustapha yace ba guba tsohon shugaban kasar ya ci ba

– Manjo Al-Mustapha kuma yace ba ‘Yan mata ne ajalin na sa baDoa

Al-Mustapha yace tun da Abacha ya gaisa da tawagar Yasir Arafat ya fara jin ba daidai ba

Dogarin na Abacha yace sharri ne ace 'Yan mata su ka kashe tsohon Shugaban

Kusan 20 kenan da rasuwar Janar Sani Abacha

Bayan shekaru kusan 20: Al-Mustapha ya bayyana abin da ya kashe Abacha
Tsohon Shugaban kasa Sojan yaki Janar Abacha

Dogarin tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha watau Manjo Hamzah Al-Mustapha ya bayyana abin da ya kashe mai gidan sa inda ya karyata cewa guba ya ci ko wai mata ne ajalin tsohon Shugaban kasan na Soji kusan shekaru 20 da suka wuce.

KU KARANTA: Inyamurai: Jami'an tsaro na neman matasan Arewa

Bayan shekaru kusan 20: Al-Mustapha ya bayyana abin da ya kashe Abacha
Dogarin Abacha Manjo Hamzah Al-Mustapha

Al-Mustapha yace tun bayan da tsohon Shugaban kasar Falastin watau Yaseer Arafat ya ziyarci Janar Sani Abacha ya ga an fara samun canji a jikin sa. Bayan ‘dan kankanin lokaci kafin ayi wani abu kenan dai sai Janar din ya kwanta wanda hakan ya kai ga ajalin sa.

A bayan can kun ji labari cewa Dogarin tsohon shugaban kasar ya kafa sabuwar Jam’iyya mai suna Green Party of Nigeria watau GPN. Tsohon Dogarin yace Jam’iyyar GPN ce mafita a Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jama'a su na dandazo domin zuwa Garin Nnamdi Kanu

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng