Garabasa: Ina mai neman gafara da biyan bukata cikin watan Ramadan
– An shiga kwamakin goman karshe a cikin wannan wata
– A yanzu ne za a dace da daren Lailatul Qadr mai albarka
– Ana kuma son a shiga ibadar I’itikafi a halin yanzu
Kun san cewa akwai lada ga wanda ya samu yin I’itikafi a cikin wannan wata. Manzon Allah SWT ya kan yi wannan ibada a masallacin sa. Ana so Musulmai su dage domin su dace da daren Lailatul Qadr.
Akwai Hadisi daga Manzon Allah SAW da ke cewa duk wanda yayi I’itikafi a kwanaki goma na karshen Ramadan ba zai shiga wutar Jahannama ba. Wannan Hadisi dai Imam Tabarani ya kawo shi.
KU KARANTA: Falalar da ke cikin daren Lailatul Qadr
Haka kuma ana sa ran ganin daren nan mai albarka a cikin ‘yan kwanakin nan, Manzon Allah ya tabbatar da cewa lallai za a samu wannan Lailatul Qadr a cikin dararen da mu ka shiga kuma musamman a kwanaki na mara watau daren 21, 23, 25, 27 da kuma daren azumi na 29.
A yau dai da mu ke magana muna daren 21 ne don haka ana sai daren ya shigo a wannan rana. A wannan dare ne dai Allah zai yafewa bayin sa da su ka nemi gafara.
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Har yanzu Najeriya na da wani matsayi a Afrika ?
Asali: Legit.ng